Shi kuna neman kalaman soyayya masu dadi da kanyo hankalin masoya? toh kun zo a sa'a. A wannan shafin, mun jero mako Kalaman so masu dadi guda 200. Guda 100 ga saurayi, guda 100 ga budurwa.
Kalaman Soyayya Zuwa ga Saurayi
- Kasan mene nake tinawa duk idan naganka, lokacin bamu fara soyayya ba; sai dai na wuce ka wuce ko sannu bata hadamu, amma gashi yanzu munzama daya. Rayuwa kenan.
- Haryanzu mamaki nakeyi. Duk da kunyar danake da ita, na iya kallar fuskar ka nace maka ina kaunarka. Gaskiya kam, soyayya nada karfi.
- Masoyina, akwai wata sirri da banfada maka ba; kana tinanin kaine kafara sona, amma maganar gaskiya tunkafin kafara kaunata nafara kaunarka, sai dai kuma bansan ta yadda zan sanar da kai bane sai gashi ka hutace ni. Kaina daban ne acikin samarai.
- Kana inane masoyina? Tun daga lokacin da muka rabu haryanzu zuciyata ta kasa samun sukuni. Ni yanzu muryar ka nakeson ji. Ka kirani yanzu kada zuciyata ta tsaya.
- Ikon Allah! Bantaba tinanin akwai wata lokaci wanda ni dakai zamuyi soyayya ba. Kasancewa tare dakai muradin zuciya ta ce, amma kuma bansan ta yadda zanfara ba. Amma cikin ikon mahalicci, muna tare.
- Duk sanda naji kawayena suna magana akan soyayya, gani nake kamar suna cutar dani soboda bantaba tinanin zanyi soyayya dawani yanzu ba. Amma daga shigowarka rayuwata, nazamo sarauniya mai fada aji a fannin soyayya. Tunda nazama sarauniya, kaga kaima kazama sarki.
- Kafin haduwar mu dakai, babu maganar dake bata mun rai kamar naji ana magana akan soyayya, amma yanzu nishadi nake shiga matuka idan ana maganar soyayya akusa dani. Kaine kazo mun da wannan sauyin cikin rayuwa. Ina kaunarka hubbi na.
- Ni haryanzu bansan da wani suna ringa kiranka ba, duk sunan dana zaba sai naji wata tana kiran saurayi dashi. Ni gaskiya kishi nakeyi, inaso na saka maka suna wanda nikadai zanriga kiranka da ita.
- Na tambayeka mana habibina, inda ace ban amince maka ba lokacin da kazo mun da maganar so, mene zakayi a wannan lokacin? Inaso nasani.
- Gani nake kamar kayi mun asiri, wannan soyayyar danake maka bazai misaltu ba. Babu abunda ke faranta mun rai kamar naji muryarka. Ita kadai ce sinadarin da zuciyata ke bukata yanzu.
- Ni yanzu mamaki nakeyi, kafin na hadu da kai, karfe 9 na dare na kwanta. Amma tunda kashigo cikin rayuwata nadaina bacci da wuri. Duk abunda ya sameni akwai sa hannun ka aciki. Har nabaka dariya ko? Karka damu babu abunda zai sa meni.
- Abunda bansani ba shine, zuciyata ke sonka ko kuma ruhina, duk sanda nayi kokarin daina tinanin ka, sai hankalina yanemi tashi soboda kashige cikinta ka samar wa kanka mazauni. Ga shawara kyauta, kazauna da kyau karka fadi.
- Nasan zakayi mamakin ganin sakona a wannan lokacin, amma babu yadda na iya ne dole sai nayi hakan hankalina zai kwanta. Nayi na kwanta nakasa kwanciya, bacci yaki zuwa duk soboda tinaninka. Idan banyi bacci ba kaima bazakayi ba.
- Shalelena, yaushe rabon danayi maka shagwaba? Gaskiya an kwana biyu, karka damu zan daura daga inda na tsaya. Amma fa sai kayi hakuri dani soboda na koyo wasu abubuwan.
- Duk sanda nake kewarka, sai naji kamar nazo gidan ku naganka, amma kuma hakan bazai yu ba. Kasan me nakeso dakai? Ka kwashe hayanka kadawo gidanmu da zama masoyina. Ka ga kullin zanganka iya yadda nake so.
- Farin ciki marar yankewa, nishadi, walwala, annanshuwa, kwarin gwiwa, sune abubuwan danake fuskanta tunda kashigo cikin rayuwata. Tunda kashigo rayuwata mukayi hannun riga da damuwa. Nima inaso na faranta maka kamar yadda ka faranta mun.
- Masoyina, meyasa baka zo gareni tun shekarun baya ba? Nashiga kunci launi daban daban, hali mara dadi, inda kana rayuwata awannan lokacin ai bazan shiga ba. Kasancewarka akusa dani kawai kwarin gwiwa ce.
- Bara nafada maka wani abu game da muryarka; aduk sanda nake cikin kunci, muryarka kadai zai iya magance mun wannan kuncin.
- Ina cikin wani hali kuma kai kadai ne zaka iya magance mun ita. Fuskarka kawai nakeson gani inji salama. Aduk sanda baka kusa dani, sai naji nakosa naganka.
- Wani tinani nakeyi, me zai hana wata rana mufita yawon shakatawa dani dakai. Muje wurin da babu mutane sai tsirrai da kuma tsunsaye dan rera mana wakar soyayya. Hakan tayi maka dadi ko?
- Nasan yanzu kana gani kamar bana kaunarka, amma gaskiyar magana soyayyar danake maka bana wa kaina. Duk wani hukunci danaka yankewa acikin rayuwata, sai da tinaninka aciki.
- Kasan ance yana da kyau duk abunda mutum zai aikata, ya duba mafitarsa. Kaine mafita ta, duk abunda zanyi babu kai aciki, wannan abu baya cika. Mafitata tana tare da kai. Acikin rayuwata, kai ne cikan lamari ne.
- Gaskiya yakamata naje nagana da M. shareef dan yakoya mun waka. Kaga sai ka rage jin wakokin wasu chan don gaskiya ina matukar kishi da hakan. Zuciyata tana ra’ayinka.
- Kishin da nake maka ce tasaka haryanzu ban gabatar dakai awajen kawayena ba. Duk abunda zai saka wata ya’ mace ta kalleka, banaso. Inso samune, ka kulle fuskarka yadda nikadai zanringa ganinsa. Kasan meyasa? Soboda hakan muradina ne.
- Gaskiya kai na daban ne, wato ka shigo cikin rayuwata ka saka makulli ka kulle ta ka hana kowa shiga cikin ta. Hakan ya nuna kaine ka chanchanci zama acikinta. Zuciyata tana maraba da zuwanka cikinta.
- Hubbina, nabaka amanar zuciyata da duk abunda ke cikinta har da kai. Ka kula mun da ita tamkar yadda kake kula da lafiyarka. Idan kayi mun hakan, daya daga cikin muradaina ya cika kuma zan kasance cikin farin ciki.
- Duk wanda yayi kokarin rabani da kai zai ga tashin hankalina, tsakanina dakai babu wanda za iya shiga. Irin kaunar danake maka, nikaina har mamaki nakeyi. Wasu lokutan sai naga kamar mafarki nakeyi. Gaskiya ka iya allonka.
- Ni gaskiya bazan iya soyayya da namiji kamarka ba kayi hakuri. Inda amsar dana baka kenan bayan kazo mun da kudurinka, wani hali zaka shiga? Zanso naganka kana kuka nayi dariya sai nayi maka tausa.
- Akwai wata tinanin dana dade ina yi amma kuma zuwanka ta yanke mun wannan tinanin; nayi samarai abaya wanda karamin abu sai su tafi kuma basu dawowa. Hakan yasa nafara amfani da Kalmar “halinsu ne” amma ka nuna mun kai ba irinsu bane.
- Kasancewa tare dakai yana daya daga cikin abunda ke samar wa rayuwata fa’ida, natsuwa da kuma nishadi. Duk randa aka ce baka akusa dani, wani hali zanshiga!
- Ubangiji ya turo mun masoyi irin wanda nadade ina bida, nadade ina nema, wanda na dade ina mafarkin samu, na dauki lokaci mai tsawo ina jiran zuwanka. Sannunka da zuwa hubbina.
- Kamar yadda taurari ke haskaka sararain samaniya wacce ke samar da haske garemu duk dare, haka soyayya da kulawarka ta samar da haske da natsuwa acikin zuciyata.
- Kasan mene ke burgeni game dakai? Iya magana; yanayin zanchenka, fadar kalamanka, da kuma muryarka sun zame mun kariya daga shiga kunci ko damuwa. Da kasan irin farin cikin da nake shiga duk sanda kake magana, da kullin idan muna magana da bazaka tsaya ba.
- Masoyina, kawayena sun fara kishi dakai fa, sunce yanzu bana samun lokaci kamar yadda nake samu abaya. Kalma daya nagayamasu, ku kasance tare da wanda ke faranta maku. Nima hakan nasamu awurinka.
- Duk idan natina akwai ranar da zan wayi gari baka akusa dani zamuyi nesa da juna, sai nazama abun tausayi. Yanzu idan baka nan, waye zai ringa kawar mun da damuwa kwatankwacin yadda kakeyi?
- Ni yanzu ko naje makaranta ban fahimtar komai, idan na kalli allon karatu, hotonka nake gani, haka zalika idan na kalli takardata, itama haka. Kewarka kawai nakeyi yanzu. Wai yaushe zaka dawo ne habibina?
- Ni yanzu bani da wata damuwa agabana daya wuce na sanya farin ciki kamar yadda kaima kayi. Duk abunda kasan zai sanya ka farin ciki, shine abunda zanyi.
- Masoyina dafatan ka tashi lafiya? Yau natashi cikin damuwa da bacin rai, nikaina bansan me ya sa hakan ba. Shin zaka iya zuwa naganka soboda nasan dana ganka komai zai wuce.
- Duk sunan da nake so nakira ka ita, sai naji ta abakin wasu, sunan da zan sakamaka bayan ni, banso kowa ya kiraka da ita. Har yan gidanku ma.
- Kasan meyasa nake kara son kasancewa kusa da kai? Soboda tundaga ranar da muka hadu da kai, sai na karu da wani ilmi ko na addini kona ilimin zamantakewar rayuwa. Kai annuri ne ga rayuwata.
- Dama yanayin da mutum ke shiga kenan aduk sanda baya tare da masoyinsa, abu kamar wasa amma gashi yana neman yazama abu babba. Ba dan halina ba, ina mai neman afuwa hubbina, kadawo gareni. Hukuncin ya isa haka.
- Ni haryanzu akwai wani abunda ke daure mun kai, meyasa duk sanda muke tare da kai bazan iya boye jindadi na ba. Kullin sai nayi yunkurin yin hakan, amma kuma baya yuwa kodai akwai abunda kayi ne?
- Masoyina kamar yadda kafara wannan jarrabawan lafiya, hakan zaka gama lafiya, nasara taka ce, bazakayi kasa a gwiwa ba. Ubangiji ya tabbatar mana da hakan.
- Bayan nazari sosai da tinani akan wanene kai, na yanke hukuncin baka gurbi da mazauni a cikin zuciyata. Dafatan dai bazakayi wasa da wannan damar ba.
- Abaya nayi tinanin furta Kalmar “ina kaunarka” kadai ke tabbatar daso. Amma kuma bayan haduwar mu dakai na fahimci cewa ta wuce hakan. Burina naga na kyautata maka, muradin jin muryarka kullin, da kuma san ganinka akusa, sune abunda nasanya wa raina.
- Ina ganin yadda kawaye na suke soyayya, amma bantaba sanin zan dandani dadin soyayya fiye da wacce suke ciki ba sai da kaddara ta hadani da kai. Ina matukar martaba kasancewarka a zuciyata.
- Lokacin boye boye ta wuce; nafada maka wani abu? A ranar dana fara ganin ka tinanina ta kasa tsayawa waje daya. Afarko na dauki abun wasa amma abun ya nemi yafi karfina. Abun daya bani mamaki shine abunda na boye acikin zuciyata kazo mun da ita. Shiyasa ban tsaya wasa ba. Kai gwanina ne.
- Ance mutane sukan iya yin komai soboda soyayya amma banda ni acikin wadannan mutanen. Soboda ni ina da abu guda daya da bazan iyayi ba. Wannan abun shine rabuwa da kai. Matukar ina numfashi, babu abunda zai saka na rabu da kai. Na daukar maka wannan alkawarin har cikin ruhina.
- Gashi safiya tayi banga sakonka ba, masoyina kana lafiya kuwa? Ka sakani cikin damuwa. Dan Allah kayi mun magana ko hankalina zai kwanta. Ina jirar sakonka yanzu.
- Yanzu dai nafara jin bacci zan kwanta, ina so kaima ka kwanta kuma kayi mun alkawarin zaka kula mun da kanka. Kuma kayi mafarki akan rayuwar mu nan gaba tare gobe ka bani labari. Karfa ka manta habibina.
- Sannun ka da war haka masoyina, dafatan kana cikin koshin lafiya? Shalelenka tana ta kewarka. Ka kula mun da kanka sosai.
- Masoyina, barka da tashi daga bacci, dafatan kayi bacci mai dadi? Ina yi maka fatan alkhairi a wannan safiyar. Nasan yanzu zaka wuce makaranta, banda kallon mata a hanya kuma amaida hankali sosai.
- Kana ina masoyina? Kasan yadda nakeji kuwa matukar banganka ba? Tun safiya nake zuwa kusa da ajinku ko zanganka, amma baka nan. Fatan dai komai lafiya?
- Natashi da safen nan cikin farin cikin da bansan dalilin ta ba. Kodai wani abun alheri zai faru a tsakaninmu ne? Dafatan kaima kana cikin farin cikin.
- Akwai wata magana da nakeso nagayamaka amma kuma bansan ta yadda zan fade ta ba. Tunda muka fara abota dakai, na manta duk wata damuwa. Burina na kasance aduk inda kake. Na kamu da kaunarka.
- Nifa yanzu nazama hajiya babba, kasan meyasa, nasamu zuciyar da nikadai ke mulkarta. Tunda ka furtamun Kalmar kauna na manta kalar kunci.
- Damuwa ya koma nishadi, bakin ciki ya koma farin ciki, tundaga ranar da muka fara soyayya nafara fuskantar hakan. Karka rabu dani habibina.
- Hubbina, ya kake ganin rayuwarmu zata kasance nan gaba? Farin ciki, natsuwar zuciya, kulawa da juna, sanya murmushi a zukatan juna , duk su nake hangowa. A daular zuciyata, kaine sarki.
- Duk sanda na bude baki nace maka ina kaunarka, ba iya nan na tsaya ba, kewarka babban damuwa ce awurina. Karkayi nesa da zuciyata.
- Da’ace sai na biya kudi zanyi soyayya dakai, dana fara adashe tunda dadewa soboda nasameka cikin sauki.
- Matukar kana cikin nishadi da walwala, nima ina cikinta idan sabanin hakan tazo, ina tare dakai duk rintsi duk wuya.
- Kamar yadda shuka ke bukatar hasken rana da ruwa dan samun rayuwa mai inganci, haka rayuwata take bukatar ka acikinta.
- Mutum da abinci ba’a iya rabasu, haka zalika abunda nake ji akanka acikin zuciyata, babu wanda zai iya chanza wannan abu. Ka kula mun da mazaunina.
- Barka da wannan lokaci mai gadin mazaunina. Nabaka dariya ko? Karka damu nima ai gadin taka mazaunin nakeyi.
- Duk sanda na kalli fuskarka, sai natina lokacin ina yarinya. Kasan meyasa? Soboda alokacin ina yarinya, irin kulawar da nasamu, irinta ka samar mun. Gani nake kamar kazo cikin rayuwata ka daura daga inda aka tsaya a baya.
- Bara nafada maka wani abun ban dariya, ina daukan lokaci mai tsawo banje kusa da tagar dakinmu ba. Amma ta dalilin ka, zama abakin taga tazama dabi’a ta soboda hanyar wucewarka ce.
- Ajiye mun soyayyarka ajiye mun wadata, zanzabi soyayyarka, kasan meyasa? Soboda zai iya karewa a kowani lokaci, amma kuma soyayarka mai dorewa ce. Kayi mun sosai habibina.
- Ni budurwa ce wacce kallon fina finai bai dameni ba, amma abun mamaki wai nine yanzu nake kallon kwallo. Kaga yadda soyayyarka ta chanza ni ko? Son kwallon ka tayi tasiri a kaina.
- Ina cikin farin ciki sosai soboda nafara cinma wata buri a rayuwa ta. Rabon da naganka cikin damuwa na manta. Muraduna sun fara cika.
- Tun safe nake jiran sakonka amma gashi dare yayi ma banji sakonka ba. Inaso kasani kullin kana cikin tinanin na. Ina kaunar ka hubbina.
- Bara nafada maka wani abun dariya, lissafi yana matukar wahalar dani a makaranta. Amma duk sanda kace mun zakazo, kwararriyar mai lissafi nake zama. Soboda kosawa naganka.
- Zuciyata kiran sunanka take tun safiyar yau. Nabata hakuri amma taki hakura. Ta kosa ta ganka. Yaushe zata ganka?
- Ba dabi;a ta bace yawan surutu, amma farin ciki da walwalar da nake samu daga wurin ka ta maidani algaita amma fa wurin surutu.
- Yanzu duk takardun makaranta na sunanka ne ajikin su, kasan meyasa? Soboda duk wanda yazo nemana, yagane cewa akwai mai wuri.
- Alokacin daka zo mun da kudurinka, nayi tinanin wasa kakeyi soboda bantaba tinanin zan burge zuciyarka ba. Gaskiya ina cikin farin ciki.
- Masoyina ka shirya, zamu fita shakawa zuwa wurin da kafi so azuciyar ka, karki damu, kanka, ta wannan hanyar nakeso nabiya ka duk wata alkhairin da ka kawo rayuwa ta.
- Masoyina, inaso kayi mun wata alfarma guda daya, ina so muryar ka tazamo wacce zanfara ji bayan natashi daga bacci duk asubanci rana. Hakan zai matukar faranta mun rai.
- Nadade ina jira ranar da zan kasance tare da wanda zai martaba kimata ta ya’ mace. Hakan muradina tun kafin yanzu, ka shigo rayuwata ka cika mun wannan muradin. Ina maraba da kasancewarka arayuwata.
- Dan kare martabarka azuciyata, sai inda karfina yakare hubibina, zan iya daina ma kowa magana amma banda wanda ke sanya farin ciki a zuciyata.
- Duk sanda na kalli fuskarka, har kishi nakeyi soboda kai din na musamman ne. murmushinka matukar kayatarwa gareta. Shiyasa nakeson kasancewarka cikin nishadi.
- Koda ban aureka a wannan duniyar ba, inaso kasani bazan taba mantawa da kai ba. Farin ciki da natsuwar da nasamu daga kulawar ka, bazan taba mantawa dashi ba.
- Kamar yadda manomi yake neman ruwan sama ido rufe, haka zuciya ta takeson ka akusa da ita.
- Tunda muka samu sabani dakai nake cikin damuwa, nayi tinanin zan iya magance rashinka acikin zuciyata cikin sauki. Amma kuma abun yazo yafi karfi na. Bazan iya rayuwa babu kai acikin ta ba. Ina kaunarka.
- Duk idan na tambaye kaina, kaine wanda ya dace dani, nan take zuciyata ta ke tabbatar mun da cewa kaine zabinta. Kuma na amince da h6akan.
- Sojoji aka sani da kare yan kasa daga miyagun mutane. Amma batare da dakaru ba, nikadai ke kare martabanka a zuciyata.
- Habibina, inaso kayi mun wata alkawari; duk maganar da mukayi tsakanina dakai, tazo mo sirri tsakaninka da zuciyarka.
- Bansan yadda gobe zata kasance ba, tunda yau muna raye, nafada maka abunda ke zuciyata, ka kula mun da kanka.
- Nakasa maida hankalina akan hidimomina, tinaninka ya sakani a agaba. Tayaya zan maganace hakan.
- Nasan kana kaunata sosai, amma da zaka iya kallon cikin zuciyata kaga irin kaunar da nake maka, da matsayina ta karu acikin zuciyarka.
- Bansan matsayina a rayuwarka ba, amma inaso ka sani cewa a rayuwata, matsayinka bazai misaltu ba.
- Duk idan wani saurayin yazo gareni da maganar so, sai naji tamkar kaine kake magana. Sai naji nakara sonka fiye da yadda nayi abaya.
- Duk sanda na saurari wakar soyayya ko na karanta takarda ko jarida, sai naji tamkar kaine gwarzo a wannan takardar.
- Na karanta wani takardar soyayya mai suna “farin cikina ya dawo” yadda kasan marubucin akanka yayi magana. Akwai kamanceceniya tsakanin lamarinka da kuma wannan littafi. Kai din na musamman ne.
- Masoyina na bude kofar zuciyata, na shreta, ya gyara komai yanzu shigowar ka kawai take jira.
- Fatan zamu kasance cikin farin ciki tare da kai har karshen rayuwar mu. Ina kaunar ka.
- Kullin ko sau dayane ka kalleni kace mun kana kewata, hakan zai sani farin ciki sosai.
- Ina kaunarka masoyina kuma hakan zai dawwama har karshen rayuwata.
- Nayi na raba kaina dakai amma kullin gazawa nakeyi soboda zuciyata bata bani damar yin hakan.
- Shin kana jin yunwa, nadafa maka abincin da kafi so, idan kazo, murmushi kawai nake bukata daga wurinka.
- Duk sanda nayi kokarin tinkarar zuciyata akan irin soyayyar da take maka, sai tabani hujjoji fiye da wanda nake da ita ahannuna. Dafatan zaka cigaba da samar mun da farin ciki.
Kalaman Soyayya Zuwa ga Budurwa
- Dafatan kina lafiya sarauniyata? Na kasa daina tinanin ki a cikin zuciya ta. Kullin cikin kewarki nake. Banaso kina yin nesa dani ko kadan soboda hakan yana sani damuwa. Irin soyayyar danake maki da mene za’a kira ta?
- Masoyiya ta, nasamu kaina cikin wata yanayi na kara kaunar ki a cikin raina. Abun kamar wasa amma yanzu yana neman yafi karfi na. Ina matukar kaunar ki. Duk wata farin cikin danake cikin ta, kece sanadin ta. Rashin ki a rayuwa ta zai matukar tabani.
- Aduk sanda nake cikin damuwa sai naga kirar ki ko sakon ki, nan take nake fita wannan damuwar. Bansan irin kallon da mutane sukeyi maki ba, amma dai masoyiyata ta daban ce a cikin mata.
- Tunda kika shigo cikin rayuwa ta nadaina shiga cikin damuwa gaba daya. Kinsan meyasa? Soboda kasancewar ki a rayuwata ta toshe duk hanyar shigowar damuwar. Ina matukar alfahari dake abar kaunata. Samun irin ki awannan zamanin abu ne mai matukar wahala. Amma kam ni na rabauta da samunki.
- Duk sanda nazo wurin ki ko kuma muna waya, sai naji kamar kada mu gama. Kinsan meyasa? Kunnuwa ta basu gajiya da jin muryar ki, idanuna basu gajiya da kallon kyakkyawar sarauniya irin ki, ita kuma zuciyata batason kina yin nesa da ita. Kaunar ki ta gama mamaye dukkan ruhi na.
- Agaskiya na kasance cikin samarai masu sa’a a wannan duniyar soboda kasancewa tare dake. Ni yanzu har kishi nakeyi da kaina soboda bana kaunar kaina kamar yadda nake kaunar ki. Hakan karamin abu ne awurina.
- Inaso nayi maki wata tambaya masoyiya ta, duk wannan shekarun bayan kina inane? Irin wannan soyayyar taki, dana same ta kafin yanzu irin damuwar da nashiga abaya da duk banshigata ba. Amma tunda yanzu kinzo, zuciyata tana maki maraba da shiga cikin ta.
- Akullin idan na zauna ina tinani, kara ganin mahimmancin ki nake gani a rayuwa ta. Akwai abubuwa da dama wanda abaya bansame su ba, amma ta sanadiyar kasancewa dake nasame su. Masoyiyata, akanki babu abunda bazan iya yi ba.
- Akullin idan natashi daga bacci, tinanin ki ke fara shiga cikin zuciya ta. Wani hali kike ciki; kina cikin farin ciki ko damuwa. Matukar ban tabbattar da hakan ba, zuciyata bata samun sukuni ko kadan. Na shigar da hakan acikin gadawalin abubuwan da kullin su nake fara kaddamarwa.
- Duk idan na shiga damuwa, sai natina nishadi da farin cikin da nake samu daga wurin ki; sai naji ni cikin salama da aminci. Maganar gaskiya, ni yanzu banda wani dalili na shiga damuwa. Samun sarauniya kamar ki ya riga ya magance komai. Sai dai nazauna nayi hamdala ga mahalicci nayi murmushi.
- Bara nagayamaki wani abu da baki sani ba. Muryar ki na dauke da wani sinadari mai sanya farin ciki a zuciyar duk wanda ya jita. Shiyasa zuciya ta bata gajiya da jin muryarki kuma take shiga damuwa matukar bata ji ta ba. Ki adana mun ita domin ita nake bukata dan kasancewa cikin farin ciki.
- Kullin idan nazauna sai zuciyata ta ringa raya mun wata tambaya; “Yanzu idan baki tare dani, wani hali zan shiga?” duk sanda wannan tinanin tazo mun, sai na shiga wani hali. Amma kuma dana tina ke din ta musamman ce, sai naji farin ciki a zuciyata. Dafatan dai bazaki yi nesa dani ba Sarauniyata?
- Duk lokacin da bamu tare dake, sai natina lokutan da muke tare, lokutan da muka samu na nishadi tare. Hakan yana taimaka mun wurin samun sukuni sosai. Zuciyata tana kewarki sosai tana bukatar ki a kusa da ita. Kizo gareta masoyiyata.
- Ta dalilin ki yanzu na daina shiga cikin damuwa ko kadan. Samun ki a rayuwata tamkar nasara ce. Kinshigo cikin rayuwata alokacin da nake bukatar mai kulawa, kuma kinyi hakan gwargwadon iyawar ki. Ina mai godiya gareki.
- Wasu lokutan nakanyi laifuka amma sai naji bandamu ba, amma kuwa duk sanda nabata maki rai, ni kaina sai na fiki shiga damuwa. Shiyasa kullin nakeson kasancewarki cikin farin ciki da walwala. Ina matukar farin cikin samun ki.
- Bamu dade da haduwa ba, amma gani nake tamkar tare muka fara rayuwa tun yarin ta. Kin shigo cikin rayuwa ta kin mayar da baki fari, kore ya zama ja, bakin ciki ya sauya zuwa farin ciki, damuwa zuwa annashuwa. Duk saurayin daya sameki a rayuwarsa ya gama samun komai.
- Kasancewarki arayuwata tamkar cinma buri ne, na rabauta da cinma wannan burin ta kasancewa tare da ke. Zan iya kiran hakan da zanen kaddara. Bantaba tinanin zan samu wannan rabon ba.
- Na tina lokacin muna yara idan kaka tana mana tatsuniya, sai ta ringa nanata wani shashi ta farin ciki da nishadi; alokacin ban fahimci mene take nufi ba, nidai nasan bana shiga cikin damuwa soboda wannan hirar nata. Amma haduwar mu dake ta saka nashiga yanayin data fi wancan. Duk sanda muke tare sai na ringa tina wancan lokacin.
- Bantaba tinanin akwai wata rana da zata zo, nazauna ina rubuta kalaman soyayya ba, amma kwarjinin ki ta saka nafara hakan. Kuma cikin farin ciki da walwala nake yin hakan. Kuma matukar muna tare zan cigaba da gudanar da hakan aduk sanda kike bukatar hakan.
- Masoyiyata, inaso kifadamun wani abu guda daya; wani abu ne yasanya kika fara so na. koma mene wannan abun, zanyi komai dan kare wannan martaban. Zan darraja soyayyar dake tsakaninmu matukar ina numfashi. Ki kula mun da kanki masoyiyata.
- Na sami kaina ina aikata wata dabi’a wacce kece musabbabin hakan, wannan dabi’an itace tinanin yadda zan faranta maki rai. Soboda matukar kina cikin farin ciki, nima ina cikin farin ciki. Inaso ki kula mun da kanki.
- Ina mai godiya gare ki masoyiyata soboda sauyin da kika zo mun da ita a rayuwata. Yanzu nakan kasance cikin farin ciki fiye da yadda nake abaya. Nasami dalilin murmushi akoda yaushe matukar tinanin ki tazo mun. Kedin ta daban ce.
- Zuwa ga ruhina, wannan sako ce daga zuciyata zuwa gareki; kin saka nagane darajar dana nake da ita, nagane mutuncin da nake da ita, hakan ai abun alfahari ne, don haka nabaki kyautar zuciya ta ki kula mun da ita.
- Aduk sanda naji wani yana fadar nasarar da ya samu, sai nayi murmushi nayi hamdala soboda nima nasami hakan. Ina matukar kaunar ki.
- Babu wani kuduri dana ke da ita face nasaka kikasance mace mafi farin cikin a wannan duniyar. Dafatan zaki bani dama dan na samar maki da hakan. Duk halin da kika sami kanki aciki, daidai take da nima ina cikin wannan halin. Ki huta gajiya sarauniyata.
- Kyawunki, baiwarki, kwazon ki, da iya magana mai dadi ne suka jawo ni gareki. Sun saka nafara ji kamar bazan iya rayuwa ba babu ke. Duk inda kike, to tabbasa akwai farin ciki da nishadi, dan tare kuke tafiya.
- Masoyiyata abar kaunata, tunda mukayi maganar haduwar mu nake ta tinaninki, nakasa dainawa. Duk soboda farin cikin zanganki.
- Duk wani dabi’a danake nema agun ya’ mace, duk kin rabauta dashi. Mene kuma zai dameni? Ina alfahari da samun ki arayuwa ta.
- Kasancewa tare dake shine hukunci mafi sauki dana taba yankewa a rayuwata. Kuma ina cikin farin ciki dan nasami nasarar kaddamar da hakan.
- Masoyiyata, inda za’a bani dama na koma baya na chanza wasu abubuwan da suka faru a rayuwata, kasancewa tare dake shine farkon abunda zan fara tabbatarwa.
- Nasan cewa ni ba gwani bane akan soyayya. Amma kuma duk wani abun da zai kawo maki nishadi a rayuwa, itace burina.
- Duk wani labarin soyayya yana da dadin ji a kunni, amma kuma tamu itace mafi soyuwar ji. Ina kaunar ki.
- Mutane da dama suna da burin da suke so su cinma a rayuwa; nima haka ina da nawa burikan, daya daga ciki shine sanya ki farin ciki matukar ina numfashi.
- Ni mallakin ki ne, babu safiya, babu rana, babu dare. Duk lokacin da kike bukatar gani na, zanzo gare ki sarauniyata.
- Masoyiyata, nazo maki da wata albishir, kece mace mafi soyuwa azuciyata. Nasan zakiyi mamakin jin hakan, amma kuma, gaskiyar maganar kenan.
- Murmushinki gareni, tafi mun ko wacce irin kadara awannan duniyar. Dan haka ki adana mun ita zuwa duk sanda nake bukatar ta.
- Wasu lokutan sai naji kamar ina mafarki, amma kuma a zahiri ba mafarki bane, wannan soyayyar ki ce ta sani hakan. Ki bani dama na faranta maki kamar yadda kika farantan rai.
- Ni ba mawaki bane, amma kuma akan soyayyar ki, babu irin wakar da bazan rera ba dan sakaki farin ciki.
- Duk sanda nayi tinanin bazan soki fiye da yadda nake ba, sai kiyi wani abunda zai saka nakara kaunarki azuciya ta, ke din gimbiya ce.
- Kinsan wani abun dake sakani farin ciki kuwa, ranar dana hadu dake mafarki na yafara cika. Ranar naji ni cikin farin ciki mara karewa.
- Duk sanda nake cikin bakin ciki, sai natina kalamanki masu dadi, kyawun ki mai kayatarwa, nan take nake manta duk wata halin da nake ciki.
- Dafatan kin tashi lafiya gimbiyata? Ga wata sako daga zuciya gareki, wannan burin da kike so ki cinma wa, ki maida hankali kiyi addua akansa, ubangijin rahama zai cika maki ita. Banso ki shiga damuwa, idan kina cikin kadai ci, ina nan duk sanda kike bukata ta.
- Tun daga ranar dana fara ganin ki nasan cewa nadaina shiga cikin damuwa. Matukar kinaso na kasance cikin farin ciki, ki kasance cikin ta.
- Akullin soyayyar ki karuwa take acikin zuciya ta. Nafara gani kamar ni wani sarkine cikin sarakuna.
- Duk sanda naje inda akwai shuke shuken fure, soyayyar dake tsakaninmu kawai nake tinawa. Karki damu wata rana zankawo maki fure mai kamshi kema kiji irin farin cikin da nake ji.
- Masoyiyata, yau natashi cikin damuwa soboda rashin ki akusa dani. Ina matukar kewarki sosai hubbi na. Ki dawo gareni abar kaunata.
- Inason ki fiye da yadda nakeson kaina. Duk idan naji wannan jimlar, gani nake kamar masu fadar ta, basu da aikin yi, amma kuma kinsaka nagane dalilin da suke fadar hakan. Soyayya dake ta saka nafara gane abubuwan da abaya bansan su ba.
- Sunar ki kamar kyawunki, muryar ki kamar surar ki, duk gwanin ban sha’awa. Samun irin wannan kadarar sai masu sa’a. Kuma ina godiya dan nasami kaina acikin su.
- Babyna. Ina kaunar ki sosai. Kizo gareni abar kauna ta soboda zuciya tasamu salama. Dafatan dai banfara takura maki ba.
- Kiyi hakuri dani idan na cika zakewa. Nikaina bansan ina yin hakan ba. Soyayyar kice ke aiki. Ki zo muje burnin masoya dan akwai nishadi marar karewa achan.
- Idan aka ambaci sunan ki a inda nake, sai naji wani farin ciki ya ratsa mun zuciyata soboda an ambaci suna mai tausasawa a kunnuwa.
- Sunani ki nusaybatou, gashi kina saka mutane nishadi aduk sanda kuke tare. Gaskiya ansaka maki sunan daya kamace ki.
- Ni haryanzu mamaki nakeyi akan wasu abubuwan danake aikatawa. Abubuwan danake ganin bazan iya ba, yanzu su nake yi. Kin chanza ni matuka. Dama haka soyayya take?
- Kinsan wani abun mamaki, yanzu zuciya ta fushi take dani akanki. Soboda nayi jinkiri wajen samar mata da farin cikin ta.
- Gimbiyata, aduk sanda na bude baki na nace maki, ina kaunarki, to ba’a iya baki na tsaya; ta shafi zuciyata da ruhina baki daya.
- Samar maki da farin ciki ya zamo abu na farko dana saka agabana; dan haka inaso kisanar dani duk wani abu wanda kikeso wanda zai saka ki kasance cikin farin ciki.
- Akullin soyayyarki kara ratsa zuciyata yake. Babu abunda ke sakani farin ciki face nagan ki kina murmushi. Matukar nasami hakan, burina ta farko ta cika.
- Kinsan wani abu? Nayi tinanin zan iya wuni daya ba tare da naji muryarki ba, bayan nayi hakan sai nakara gane mahimmancin ki a rayuwa ta.
- Tanason ka kuwa? Tambayar da abokaina suke yi mun kenan kullin. Amsata ga wannan tambayar shine, kamar yadda nakeson ki, haka kike sona. Amma haryanzu sun kasa yarda.
- Babban burina a wannan soyayyar itace nazamo sanadiyar murmushin da zakiyi, nishadi da farin cikin da zaki shiga. Daga nan kuma mu kare rayuwar mu cikin aminci. Dafatan zansamu hakan?
- Gimbiyata da zan iya baki wata babbar kyauta, dana ce maki ki kalli cikin idanuna kiga irin kaunar da nake maki. Har cikin zuciyata, babu wata mace da ta taba sakani farin ciki kamar yadda kika sani.
- Ni ba wani sarauta bane akaina, amma soyayyar da kike nuna mun ta saka ina jin kaina kamar wani sarki. Gaskiya zanyi kyau da sarauta amma ta zuciyar ki. Kinga ni sarki, ke kuma gimbiya ta, duk abunda kikeso shi za’ayi.
- Akwai wani abu da akullin idan na tina, sai hankalina ya tashi; idan aka wayi gari bamu tare, wani irin hali zamu shiga? Gaskiya zanji ba dadi. Babu abunda kaddara batayi. Ki kula mun da kanki shalelena.
- Ubangiji ya halicci mutane daban daban, kowa da abun da ya rike a rayuwar sa wanda take bashi kwarin gwiwar kaddamar da hidindimu. Amma kuma ni, duk wata kwarin gwiwa ta, daga gare ki take zuwa.
- Tunda muka hadu dake nasami dalilin tashi duk safiya da wuri, kinsan meyasa? Soboda inaso na zama wanda zai fara jin muryar ki a duk safiya. Jin muryarki kafin na kwanta da kuma bayan na tashi daga bacci muradin zuciyata ne.
- Bazan iya misalta irin yanayin dana nake shiga ba, aduk sanda kika kalleni kikayi murmushi. Nidai abunda nasani, murmushinki nada matukar kayatarwa. Dan haka hubbina, inaso ki adana mun sinadarin farin cikin rayuwata.
- Kinsan meyasa nake yin shiru na natsu duk sanda kike magana? Soboda muryarki na samar da natsuwa kamar yadda take da natsuwa.
- Farin ciki tsakanin juna muradi ne ga duk masoyan kwarai. Ba wani abu babba nayi ba gashi na kasance cikin wannan masoyan na kwarai. Kece musabbabin hakan.
- Akace mace zinariya, kadara ga mai ita. Inji turawa suka ce “Treasure in the sky” kinsan mene hakan ke nufi? Samun ki a rayuwata, kamar kadara ce a cikin sararin samaniya tazo gareni kuma na amsheta hannu biyu. Ki kula mun da kanki.
- Hubbina, kinshigo cikin rayuwata alokacin da bana samun kulawa, kin kula dani tamkar yadda kike wa kanki. Ina so kibani dama na kyauta maki kwatankwacin yadda kika mun. Ina matukar alfahari da samunki a rayuwata.
- Muradin zuciya ta itace kullin naganki cikin farin ciki da nishadi. Duk sabanin hakan zai saka na shiga damuwa. Kasancewarki cikin farin ciki lafiya ce ga rayuwata.
- Duk idan naji wani yana magana akan yaudarar da wata ta mai, abunda nake sakawa acikin zuciyata, shine haryanzu bai hadu da sarauniya irinki bane. Matukar ya hadu da mace kamar ki, duk zai manta wannan maganar tasa.
- Ina so kifadamun abunda nakeyi wanda ke burge ki, koma mene ne wannan abun, nayi maki alkawarin kara yinsa aduk sanda kike bukatar hakan. Ina matukar kewarki.
- Bamu dade da rabuwa ba, amma jinake kamar shekaru sun wuce bamu tare. Masana sunyi gaskiya da suka ce, ba’a sanin amfanin mutum sai babu shi. Na dandana zafin rashin ki akusa dani. Ki dawo gareni masoyiyata.
- Duk idan na kalli wata mace ba ke ba, sai naji haushi soboda wacce yakamata na kalla ba ita na kalla ba. Ina ganin kasa kawai zanfara kallo idan ina tafiya.
- Duk idan nazo wurinki, bayan mun rabu, tafiya nake da kafata, soboda inaji kamar muna tare. Samun budurwa irinki, akan kira hakan da zanen kaddara.
- Abu guda daya wacce zai saka hankalina ya tashi shine nayi wuni daya batare da naganki ba, banji muryarki ba. Cikin kunci da bacin rai zan wuni. Shiyasa kullin nake iya bakin kokari na nasamar wa kaina da hakan.
- Inda so samune, duk safiya zanzo angwarku na tsaya, idan kinfito naganki sai na wuce, da rana ma nazo na ganki sa’an nan kuma nayi hakan daddare. Zuciya ta, zatafi samun sukuni akan hakan. Wannan ba komai bace face soyayya.
- Masoyiyata, sarauniyata, hubbina, ruhina, duk wannan sunaye ne wanda mutane ke kiran budurwarsu da ita, amma kuma ni duk basu mun ba; na kiraki shalelena. Gaskiya yakamata nafara maki shagwaba.
- Yanzu dai nazama sarki ba tare da an nadamun sarauta ba. Duk nasami hakan ne soboda kasancewa da sarauniya irin ki. Sarauniyar kyau, ga zakin murya, ga iya magana. Komai kin hada.
- Duk sanda nake kewarki, sai na dauko wayata na duba sakonnin da kika turo mun, sai naji dadi acikin ruhina. Yaushe zaki dawo gareni?
- Bansan tinanin mene kike yi akaina ba, amma inaso ki gane wani abu guda daya, aduk sanda natina ina da ke agefe na, sai naji ni cikin nishadi da walwala. Dafatan zaki cigaba da zama akusa dani?
- Ni yanzu bani da wata damuwa a zuciyata face naga na kyautata maki, na sakaki nishadi da murmushi. So duk wani abu da nakeyi yanzu, dan farin cikin ki nake yin ta.
- Duk wanda bai soyayya da sarauniya kamar ki, an barshi a baya sosai. Rabon dana shiga irin farin cikin da kika sakani, tun kafin na hadu dake. Kuma zan cigaba da kasancewa cikinta matukar muna tare.
- Sai kiji wasu samaran suna cewa basu san mene ne dadi ba a cikin soyayya ba. Dan haka bazasu ba wa kansu wahala ba. Sai nayi murmushi, kinsan meyasa? Soboda haryanzu, basu dandani irin zuman dake cikin soyayya ba. Nidai kin dandana mun kuma na lasa.
- Bansan yadda ake soyayya ba kafin haduwar mu, amma gashi yanzu kinsaka nagane mahimmancin soyayya. Ina godiya sarauniyar kyau.
- Ko kinsan meyasa fure ke dauke da jar kala? Hassada take da kyawun da kike dashi. Jinake kamar na rungumeki ki daura hannun ki akan zuciya ta kiji irin bugun da take maki.
- Duk wata bugu da zuciya ta take yi, tare da soyayyar ki take hakan. Matukar babu ke acikin ta, zata samu matsala. Na mallaka maki zuciyata hannu biyu aminiyata.
- Duk wani namijin da kika gani awurin budurwa, akwai abunda takeyi wanda ya burge shi har yaji ta kwanta masa a rai; yanayin rayuwar ki, iliminki da kwazonki wajen iya sarrafa magana ce suka jawo ni gareki masoyiya ta.
- Tun daga ranar da muka fara soyayya har zuwa yau, kullin kara gane mahimmancin soyayya da mace mai kirki nake. Duk hakan tasamu ne soboda ke.
- Da’a ce ta dalilin wata muka hadu dake, da na girmamata tamkar ahalina soboda tayi sanadiyyyar haduwa ta da gimbiyar dana dade ina muradi.
- Bansan ya zaki dauki wannan maganar tawa ba, amma har cikin zuciya ta, ruhina, ina son zaman ki akusa dani a koda yaushe.
- Inaso kiyi mun wata alkawari guda daya; Na kasance cikin farin ciki da nishadi ta dalilin ki, kuma hakan zai cigaba da dorewa ne matukar kema kina cikin farin cikin, don haka ina so kiyi mun alkawarin zaki kasance cikin farin ciki duk rintsi.
- Ko abinci zanci yanzu baki akusa dani, sai naji abincin ya ginsan. Yanzu abinci ya nuna, zaki zo mu ci tare?
- Mamata tace mun nazo gida tare da shalelen da ta saka danta farin ciki, shin zakizo ki gaishe da ita. Don kuwa kullin sai nabata labarin ki.
- Akwai abunda turawa suka kira da “Treasure” ma’anarsa, wata kadara ce mai wuyar samu. Duk wanda aka gani da ita, ba karamar wahala yasha ba kafin ya sameta, amma kuma abun mamakin anan itace, cikin sauki nasamu hakan. Ina matukar godiya gareki hubbina.
- Yau wanki nakeyi agida kuma ina ji na da karf, shin zaki kawo naki na tayaki ne? Zan iya yin komai soboda farin cikin ki.
- Yanzu mubar maganar wasa, idan muka hadu dake a wata duniyar nace ina kaunar ki, zaki amince dani ko kuma sabanin hakan?
- Bayan mungama waya na kwanta bacci, nayi mafarkin ki. Kuma abun alheri ya sameki a wannan mafarkin. Kiyi mun murmushi sai na fada maki.
- Akwai abunda ke damuna acikin zuciyata, nayi kokarin danne ta, amma kuma kullin hakan gagara ta yakeyi. Na kamu da kaunar ki alokacin da banyi zato ba. Mene kike ganin ya kamata nayi yanzu? Inda haka nace maki lokacin dana zo maki da kudurin soyayya dake, zaki amince mun?
Comments
Post a Comment