Fadawa budurwar ka ko saurayin ki kalaman soyayya masu dadi na da matukan mahinmanci sabo da yana kara dankon so. Akwai ira iran kalaman soyayya. Wasu kalaman soyayyan na nishadantarwa. Wasu kuma masu sa dariya ne.
Amma ba kowa bane keda lokacin rairaya zafafan kalaman so ba. Sa boda haka, mun zanna mun rubuta muku zafafan kalaman soyayya guda 200 biyu. Daga ciki, Akwai kalaman soyayya masu dadi da ratsa jiki. Akwai masu sa dariya, sa Kewa da kunani. Mun raba su Kashi biyu — Kalaman soyayya na maza da kuma na mata.
Kalaman Soyayya Na Maza Zuwa Ga Budurwa
A matsayin ka na saurayi, ya ka mata ka iya razana budurwar ka da kalaman soyayya soyayya. Idan ko ba haka ba, sai ka ringa wahala wani ya sace maka ita da kalaman so. Karanta kalaman so wainda muka jera maku.
Kalaman So Masu Ɗaɗi
Soyayyar ki tasa kullin cikin farin ciki nake dawwama. Ke ce dalilin duk farin ciki da murmushi cikin rayuwa ta. Ke ce mace mafi natsuwa a cikin matan da nariga nasani. Na gode da kasancewa saurayi mafi soyuwa a zuciyar ki. Ina son ki sosai!
Duk yadda nake shagaltuwa, zuciya ta ba ta mantawa ta tuna mun da cewa sarauniya ta na buƙata ta. Da yawan kwanaki na tafiya, hakan yasa soyayyar ki na kara girmama acikin zuciya ta. Kece sarauniyar zuciya ta.
Ban taba tunanin zan samu budurwa irinki acikin rayuwa ta. Ban taba tunanin zan samu mace mai kula da sa natsuwa kamar yadda kike ba. Amma cikin ikon Ubangiji, duk ya sa na gane cewa ƙauna ta gaske tana wanzu wa kuma na yi sa'a matuƙa da samunki a rayuwa ta.
Kin ba ni dalilin rayuwa, mafarki, da kuma jindadi. Kin sanya kwanakina sun kasance cikin farin ciki da natsuwa. Na gode da kasance wa mace guda daya ta fahimci yaron zuciya ta. Ina son ki abar ƙaunata.
Ba na son duniya, ba na son sararin sama, ba na son wata, zuciya ta da hankalina yana samun natsuwa be a duk sanda nake tare da ke a zahiri ko a baɗini. Ina son ki fiye da yadda kike tunani, abar ƙaunata ! Kece sarauniyar zuciya ta kuma son rayuwa ta, kuma ba zan iya tunanin rayuwata babu ke a cikinta ba.
Kyawun ki, hazakar ki, da kyautatawar ki, suna sa na kamu da sonki kowace rana! Ke ce ta fari a zuciya ta. Ba zan iya dai na son ki ba domin shi ne kawai abin da na kware a kai, kuma shi ne kawai dalilin da ya sa aka aiko ni nan duniya. Ina son ki a rayuwa ta dan kasance wa cikin farin ciki.
Kasancewar ki a rayuwata albarka ce ta rayuwa ta. Kece kyautar da ban taɓa kuskura in roƙa ba. Soyayyar da kika mun ta fi karfin tinani na. Wani lokaci ina jin kamar ina mafarki, amma sai na gane cewa duk gaskiya ne kuma ni ɗaya ne mai sa'a a cikin wannan kyakkyawar duniya. Kinsan meyasa? Soboda nasami budurwa wacce take sona take son kasance wa tare dani. Na gode da kasancewa tawa!
Ina gode wa Ubangiji kowace rana domin ya amsa addu'ata kuma ya ba ni budurwa mafi kyau a duniya. Ba zan iya taimakon kaina ba a lokacin da tinanin ki yayi mun yawa ba. Sai naji kamar nazo na tare a gidan ku, dan na rinka ganin ki a Kullin. Ke ce mafi kyawun mace da na taɓa sani. Ina son ki fiye da komai a rayuwa!
Ina jin kamar mutumin da ya fi kowa sa'a soboda ina da budurwa irinki a rayuwa ta mai kula dani, mai sani nishaɗi da kuma sani farin ciki. Allah ya albarkace ki da mu baki daya. Murmushin ki shine ladan da nake son samu kowace rana. Shi ne kawai muradi ba a kullin.
Kina haskaka duniya ta kamar ba kowa, kuma na fi son hakan game da ke, sweetie. Ton na soyayya. Duk yadda ranata ta kasance, duk fushina da bacin raina duk shuɗe wa suke da zarar na ganki ko naji muryan ki mai ƙayatarwa. Na yi farin ciki da godiya da samun ku a rayuwata.
Duk inna tashi da safe sai zuciya ta ta ce mun kamanta wani abu. Amma sai na ƙasa tina mene. Hakan sai yasa zuciya ta tayi fushi dani, daga baya nagane cewa zuciya ta muryan ki kawai take son ji ba komai ba. Ina sonki, Shin kina sona kamar yadda nake son ki?
Gaskiya kam nayi sa'a a rayuwa ta dan samun budurwa irinki abu ne mai matuƙar wuya. Inna ga yadda abokaina da yan matansu ke soyayyar su, sai abin ya bani dariya don kuwa kap matan su babu kamar ki. Har kishi suke akanki.
Zuciya ta ta kasa natsuwa, kullin cikin tinanin ki nake duk safiya, rana, yammaci da dare. Ban tinanin zan iya kwana daya ban ji muryan ki ba. Soboda haka nake son kasance wa abokin rayuwar ki.
Inaso ki yi mun wani alkawari. Inaso muryanki yazama na farko da zanji inna tashi daga bacci, kuma yazamo na karshe kafin in kwanta bacci. Zaki iya yi mun hakan masoyiya ta?
Wata rana na zauna ina tinanin yadda rayuwa ta zata kasance nan gaba. Amma gaba daya lissafin baya cika. Na bi duk hanya da zan iya bi dan ganin na cin ma burina amma duk bai yu ba. A wannan lokacin ne nagane cewa kece dalilin. Ina matuƙar sonki sosai!!
Masoyiyata in maki waƙa, amma sai dai ban sani ba zaki so wakan ko ba zaki so ba. Karki damu kanki dan waƙar me yaye bakin ciki ne.
Duk in aka tambayeni daya so daya sai in ce biyu, a ganin su ban san me nake yi ba, amma babu yadda za'a yi in zama ɗaya bayan ina da sarauniya irinki a rayuwa ta mai san farin cikina, wacce bata son ganina cikin damuwa.
Duk iya yadda za'a yi ma namiji kyauta, gaskiya ni na samu. Kinsan meyasa? Dan ina da sarauniya dake kula dani sosai. Bazan iya rayuwa ba babu ke.
Sarauniya ta inaso ki faɗamun ne kike so wanda zai sa ki cikin farin ciki mai dorewa? Ni na maki alkawarin cika maki burin ki matuƙar bai fi karfina ba. Kinsan farin cikin ki shine muradi Nana fari.
Wasu suna tunanin kalmar "ina sonka shine soyayya" amma kulawan da kike nuna min yasa nagane cewa soyayya ta kunshi abubuwa dayawa. Zan yi iya bakin ƙoƙari na naga cewa na faranta maki rai a koda yaushe.
Kalaman So Masu Ratsa Jiki
Nasan kila kina tunanin zan yaudare ki dan ina haɗuwa da mata a wuraren da nake zuwa. Amma ina so ki sani cewa matsatin ki a rayuwa ta, ba zai taɓa sulwanta ba domin kuwa farin cikin ki shine jindadi na. Inaso kiyi mun alkawari guda daya, ki kula mun da kanki.
Dama masana sunce hanya mafi sauki da zaka san kaddarar rayuwar ka shine ta hayanyar samun budurwa wacce take sonka. Kuma naga alamar kaddarar rayuwa ta abun alfaharine tunda ga ki a cikin ta. Zan kula da ke sosai. Tare da ni babu abunda zaki rasa. Inaso ki sosai.
Jiya ina zaune kika so wu cewa amma sai na ƙasa sukuni soboda wata tunanin na ce mun inbiki wata tunani ba cemun inbarki kiyi tafiyarki. Gaskiya kina da kwarjini dan ba kowani namiji zai iya tarar ki ba. Na ɗade ina tinanin yadda zan tare ki amma hakan yaƙi yuwa. Amma yanzu a shirye nake na bayyana maki abunda zuciya ta ke dauke da ita. Ina sonki.
Kafin haɗuwa dake a rayuwata ina saurin bacci kuma ina makara wajen tashi. Amma shigowarki rayuwa ta yasa kullin ina makara wajen kwanciya sa'an nan kuma in tashi da wuri soboda ina so in tabbatar kina lafiya kafin in kwanta kuma da safe inji inkin tashi lafiya. Hakan shine muradina.
Da so samu ne, da a ce kullin zan ganki a kusa da ni, dana fi ko wani ɗa namji jindadi a wannan similar.
Bansaniba in akwai wanda ya taba ce maki wannan kalmar ba. Amma inaso ki sani kina da matuƙar mahimmanci a rayuwa ta.
Bansan meyasa zuciya ta bata gajiya da ganin ki ba. Kullin cikin kewarki take a koda yaushe. Gaskiya kina da matsayi babba a zuciya ta.
Duk inna zauna naji an ambaci sunan ki, naji na juwo cikin murmushi amma daga lokacin da nasan bake bace, sai naji ba ɗadi. Ina so ki rinka kasance wa kusada ni.
Kinzamo mai sani farin ciki, murmushi, jindadi, hakan yasa soyayyarki a zuciya ta ke yawaita duk bayan sa'a daya. Ya Allah yabiya maki buƙatar ki duniya da lahira.
Duk lokacin da na kalli fusƙarki, sai inyi addu'a acikin zuciyata na roki Allah yabani iko naci gaba da faranta maki dan murmushinki a koda yaushe abun ne mai matuƙar ƙayatarwa. Ina mai rokonki ki ki cigaba da murmushi dan kuwa silar farin cikin ne ga bil Adama.
Masoyiyata, babu wanda ya haskaka ni ko ya dauke ni a rayuwa kamar ki. Na gode don kasancewar ki mai tausasawa, kulawa, da kirki a gareni. Me zan yi ba tare da ke ba? A cikin mafarkina ban taɓa ganin wata in ba ke ba.
Tsawon lokuta, kin zama wani sashe mai mahimmanci a zuciya ta. A gare ni, ke kyauta ce da ke zuwa sau ɗaya a rayuwa.
Ina fatan za ki tuna kowace rana cewa kina da mahimmanci, kuma za ki iya cimma duk abin da kika yi niyyar yi. Ina faɗin haka cikin cikakken tabbaci domin na ga kin canza rayuwata. Ina son ki sosai.
Ƙaunata gare ki tana da ƙarfi kamar yadda jiki yake da jini. Idan aka waiwaya baya, ina mai matuƙar godiya don tsayawa a gefena da kasancewar ki mai bani nishaɗi da ban taɓa samu ba a wurin wata macen ba.
Me kuma zan iya tambaya banda kallon kyawawan idanunki har abada? Murmushin ki mai yaduwa yana narkar da zuciya ta da hannayena don rungumarki har abada.
Duk abinda ke faruwa a rayuwa, tunanin ki yana sa mun nutsuwa. Kasancewar kina sona duk da kasawa na Allah ne. Tunanin ki kawai yana kawar da duk wata damuwa ta. Ina son ki!
Duk sa’an da na yi tunanin ki, raina ya cika da tunanin farin ciki game da danginmu na gaba. 'Ya'yanmu za su sami mahaifiya mafi kyau a duniya, kuma don haka, ina yi muku hassada.
In akwai abin da zan taɓa buƙata kece. Don kawai in sami ki a gefena ko a cikin rana mai zafi ko lokacin sanyi, zan iya yin wani abu tare da ki kusa da ni.
Ko da a shekara 50, za mu kasance matasa da kuzari a zuciya. Na rasa kirge na sumba, runguma, da kyawawan lokutan da muka yi, kuma duk abin da zan iya yi shi ne fatan mu yi sabbin abubuwan tunawa. Na gode, abar ƙauna ta.
Kamar yadda teku ke lalata bakin teku da raƙuman ruwa, Ƙaunarki ta lalata bangon da ke kewaye da zuciya ta. Ina cikin tafiya ina rayuwa a cikin duhu, amma zuwan ki yazo da haske mai haskaka wa, kin bude idona. Ina alfahari da kasancewar ki tawa.
Kalaman So Masu ban Dariya
Ina so in koyi yadda ake yin sihiri. Sa'an nan watakila zan iya bayyana yadda soyayyar ki tasa nakeji. Har zuwa lokacin, ina son ki fiye da yadda nake son zuciya ta.
Ina mamakin wanda zan fi so fiye da ki? ko dai wata budurwar ce daban? Karki damu zolaya ce kawai. Babu wata budurwar a ko'ina bayan abar ƙaunata. Ina son ki, baby na.
Idan kin same ni ina rawa a kan hanya, kawai ki sani cewa farin ciki ne ke fitowa daga ƙaunar da kike nuna min. Karki zarge ni. Laifin son ki. Ina son ki, masoyiyata.
Idan zuciyata ta kasance kafofin watsa labarai, batu daya da ba zai daina tasowa a kai ba shine labaran soyayyar mu. A gaskiya, zuciyata tana jin daɗinsa. Ina son ki, sarauniya ta.
Kowace rana, na tashi ina tunanin ranar da zan saka zobe a waɗannan yatsun naki masu ban mamaki. Yatsu masu ban sha'awa san wanda ya samu, kin wanda ya rasa. zan iya yin duk abun da kike so nayi dan naga waɗannan yatsun naki. Ina son ki, masoyiya ta.
A gare ki, zan yi tafiya zuwa duniyar wata kuma in dawo. Zan ma iya hadiye rana in hakan ne zai sa ki kasance a gefena. Ina son ki haka.
Akwai yan mata da yawa da suke ƙoƙarin zama kamar ki, amma, a gare ni, idan ba ke ba ce, to ba ke ba ce. Ina son ki kamar yadda mutum ke son ruwa.
Kowane namiji kamar ni yana bukatar mace irin ki a rayuwar sa, kuma duk sun sami matan su. Domin nida ke daya ne kawai . Ina son ki sosai, masoyiya ta.
Ina so in yi sauran rayuwata tare da ke. Har ila yau, ina rokon Ubangiji don bani ikon kasance wa tare da ke abada. Ki ji dadin ki, tauraruwa daya tak acikin dubu, Ina son ki!.
Barkan ki masoyiya ta, Ina ta jin kina cewa ni naki ne. Kina nufin saurayinki ne ko bawanki? Abun dariya. Wasa kawai nake maki, Ina son ki sosai.
A da ina tinanin na iya soyayya, amma haɗuwar mu da ke ya nuna mun a soyayya haryanzu ba abinda nasani. Kula wan da kike nuna mun yasa na fara shagwaɓa. Dafatan dan ban taƙura maki.
Na tina lokacin muna yara, in munka ga mace da namiji suna tsaye, sai muyi ta kallansu muna cewa waɗancan me suke yi ne. Dama ashe haka suke ji a cikin zuciyar su? Gaskiya rayuwata in babu ke, akwai marsala acikin ta.
Banyin chacha, amma zuciya ta da tinanina sun sa na fara cha cha akan zan iya soyayya da ke ko bazan iya, amma sai yin nasara nake akansu. Soyayya ta gare ki abun dubawa ne.
Bansan me ke damun idanuna ba, duk inna ganki bazan iya daina kallon ki ba. Yanzu muyi wata kamarar wasa, ina son na sace zuciyarki gaba daya, kema inaso ki sace tawa. Zaki iya kuwa?
Abun dariya, alokacin ina yaro, mama na ta yawan ce mun ina kuka sosai. Kinsan me yasa nake wannan kukana? Soboda zuciya ta ce ke kewar ki.
Jiya naje bacci, sai na rungumi matashi na kuma nayi mafarkin ke nake rungumi. Nasan wata rana na nan zuwa wanda ke zan runguma inyi mafarkin matashi na.
Inaso kiyi mun wani alkawari guda daya tak. Na kulle zuciya na kuma zan baki makullin. Kema hakan ki kulle naki zuciyar kiban makullin, sai mujefa makullin a cikin teku, kinga babu ruwan mu da kowa, zamu yi soyayyar mu cikin farin ciki.
Irin san da nake maki, ko tusa kika yi, to yafi komai kamshi a wurin na. Dan Allah karki sa tunanin komai ya dame ki. Ki tina kina dani.
Wasu lokutan sai nayi tunanin inbamu haɗu ba, ya rayuwar zata kasance? Anan ne na fahimci cewa rashin ki arayuwa ta matsala ce babba.
Ban kallon wasan barƙwanci, amma nishadin da kike ban, yafi wanda masu kallon barƙwanci ke samu. Shiyasa kika ga inban ganki ba nake kamuwa da rashin lafiya.
Kalaman So Na Kewa
Zai Iya yuwa Ina da dalilin murmushi, haka zalika dalilin wasa cikin yan uwa da abokan arziki, amma kuma ina da wani abu guda daya dake ɓata mun rai, wannan abun shine rashin ganinki.
Na kanyi kewarki da safe, da rana, da kuma dare a duk lokacin da bamu tare. Dan Allah ki dawo kusa dani dan zuciya ta tasamu natsuwa. Yaushe zan ganki?
A duk lokacin da saurayi ke kewan budurwar sa, hakan na nuna cewa ita wani shashi ce a rayuwar sa, toh misali hakan nake a duk sanda bamu tare da juna. Ki kula mun da kanki hubbi ta.
A duk sanda bamu tare da juna wata cutar ke ka ni. Kinsan me sunan wannan cutar? Sunan ta cutar kewa. Ina sonki sarauniya ta.
Gaskiya ban da lafiya kuma rashin ganinki ne dalilin. bazan iya cire wa kaina wannan kaddarar ba.
Babbar abun ɓacin rai shine, a duk sanda nayi ƙoƙarin Hana zuciya ta kewarki, sai inji wani raɗaɗi yadda bantaɓa tsammani ba.
Kece dalilin farin cikina, kece dalilin nishadin da nake ciki, kece musabbabin duk wani jindadi da walwalar sa nake fuskanta. Amma gashi kinyi nesa da ni, yaushe zan ganki?
Duk lokacin da aka kira waya ta, sai nayi tunanin kece, duk lokacin da sako ya shigo waya ta, sai nayi tunanin kece, duk lokacin da aka sunanki, sai nayi tunanin kina kusa. Ina kewarki masoyiya.
Baki ɗaɗe da tafiya ba, amma meyasa zuciya ta ta kasa samun natsuwa ne. Wannan so ne na hakika. Ki kula mun da kanki.
Duk abunda na kalla, sai nayi tunanin kina cikin wannan abun, soboda ke kadai ce a cikin zuciya ta kuma ke kadai ce abokiyar rayuwa ta.
Har gori ake mun soboda wai nasa tunanin mace guda daya tak acikin zuciya ta. Amma sai dai nace masu, bazan ku gane yadda zuciya ta ke ciki ba. Kina da matukar amfani a zuciya ta.
Nayi kewarki sosai, yaushe zaki dawo ne? Zuciya ta ta kasa natsuwa.
Duk lokacin da muka rabu, sai naji kamar babu komai a cikin zuciya ta. Ke kadai nake muradi.
A kullin sai in ta kallon taurari a cikin samaniya sai naita tinanin zan ganki amma kuma saɓanin haka ke faruwa. Amma karki damu, wata rana sai labari.
Basan ta yadda zan iya faɗa maki ina sonki ba. Amma inaso duk inda kike, kisa aranki akwai wani mai sonki sosai.
Duk in kina kusa dani, farin ciki mai ɗorewa ke samu na, amma a sanda kika barni dai dai da sa'a daya, sai naji rayuwa ta chanza gaba daya.
Zama a rana guda tak ba tare da ganin ki ba dai dai yake da rana guda babu farin ciki.
Na rubuta sunanki a bangon ɗaki na, kinsan meyasa? Soboda duk inna kalla naji sauki a cikin zuciya ta.
Duk lokacin da bamu tare, sai naji zuciya ta sunan ki kawai take kira.
Ni yanzu ban bakatar abinci, ruwa har iska, ke kawai nake buƙatar gani a yanzu.
Kalaman So Masu Sa Tunani
A duk sanda na zauna sai naji kaina na nuna mun hoton wata kyakkyawar budurwa, kinsan wacece ita? Ta sace mun zuciya, kuma kece.
Wannan wani irin soyayya kike nuna mun hakan ne? Duk lokacin dana kalli wata a cikin samaniya, sai naga kamar kyawunki ya wuce na watan. Dan Allah ki kasance tawa har abada.
Bazan iya jurar rana daya tak ba tare da naganki ba. Har ji nake kamar nun fashi na zai dauke. Ke kawai nake gani duk inda na kalla.
Ƙaunar da nake maki kamar misalin zurfin koji ne wanda babu wanda yasan iya kar shi. Haka zalika nisan samaniya ma misalin irin ƙaunar danake maki ne.
A kullin inna kalle ki sai naga kamar kin kara kyau fiye da yadda nasan ki. Hakan ne yasa yana ke so nai ta kallon ki, hakan na sani nishaɗi da farin ciki.
Ina son ki, gashi dai kalma uku, amma ya hanani sukuni. Kice kina sona ko hankali na zai kwanta.
A kullin kallon kyakkyawar fuskar ki shine muradi na, jin muryan ki mai matuƙar ƙayatarwa shine farin ciki na, sanin lafiyar ki shine buri na. Kina lafiya sarauniya?
Ki zauna kiyi tinanin akan meyasa duk in kika fito kike ganin rana na kashe maki fuska, ba komai bane illa gasgata irin kyawun da Ubangiji ya maki.
A kullin burina na farko shine in kalle ki a cikin Ida nunki ince maki ina sonki amma sai in kasa soboda kyawunki da kwarjinin ki sunyi karfi a cikin zuciya ta.
Na zauna nayi tinani, nayi nazari kuma nagane cewa a cikin shashin rayuwa ta, ke ce silar dariya, murmushi da kuma farin cikin danake ciki dan haka yin abunda zuciyar ki ke so shi ne muradi na.
Lokacin da na taso, ban iya waƙa ba, amma dole na koya waƙa dan ganin hakan zai sa ki kasance cikin farin ciki da walwala.
Nasan wasu lokutan nakan baki haushi, na Kan saki fushi, na kan saki tinani akaina sosai, amma duk cire wannan a zuciyar ki ki tina abu daya, farin cikin ki shine buri na.
Nakan yi maki wasa a sanda muke tare, na kan dauke abubuwa kamar basu da mahimmanci, amma soyayyar ki a zuciya ta ya wuce misaltawa.
Abokaina su kanyi magana akan yadda soyayyar su take, amma duk yadda suke jin dadin soyayyar su, bai kai nishaɗin da nake samu ba alokacin da muke tare.
Kin kasan ce wata kyauta da na samu a rayuwar duniya wanda bazan taɓa bari ya sulwanta ba. Zanyi duk bakin ƙoƙari na na kiyaye duk abunda zai saki fushi.
Gurbin da kika rike dashi a cikin zuciya ta babu wata iya mace sa zata taba rike wa. Kina da matukar amfani a rayuwa ta.
Sarauniyar rayuwa ta, nagode da wannan farin cikin mai ɗorewa da kika kawo rayuwa ta.
Tsawon lokuta, kin zama wani sashe mai mahimmanci a zuciya ta. A gare ni, ke kyauta ce da ke zuwa sau ɗaya a rayuwa.
Kinzamo mai sani farin ciki, murmushi, jindadi, hakan yasa soyayyarki a zuciya ta ke yawaita duk bayan sa'a daya. Ya Allah yabiya maki buƙatar ki duniya da lahira.
Duk ina rubutu sai wani harafi guda daya ya fita amma kuma bansan me yasa ba, duba ga lamari da kuma nazari, sai nagane cewa kece cikar harafin. Ina sonki sosai.
Kalaman Soyayya Mata Zuwa Ga Saurayi
A matsayin ki na budurwa, kinyi asara idan har bakiyi iya fadawa saurayin ki kalaman soyayya ba. Fadawa saurayi kalaman soyayya wani salo ne na shagwaba. Kuma zai iya sa saurayin ki yaji bai’iya rayuwa in ba ke. A wannan bangaren, mun jero maku zafafan kalaman soyayya wa inda zaku iya turawa saurayin ki.
Kalaman So Masu Daɗi
Kafin in haɗu da kai, ban taba sanin yadda ake kallon mutum da murmushi ba gaira ba dalili ba.
Kasancewa tare da kai ya na daga cikin lokuta masu igantuwa a gare ni.
Ina son mu yi wauta tare. Ina son shi ka kyautata min. Ina son yin lokaci tare da kai. Ina son ka habibiy!
Ka sanya lumshe ido a cikin idona, ka sanya ƙoshiya a cikina, kuma ka shigar da soyayya a cikin zuciyata.
Soyayya ita ce wauta tare. Wanda a zahiri yake misalta dangantakarmu! Ina son ka da yawa!
Wani wuri tsakanin duk dariyarmu, dogon zance, ƴan faɗan wawa, da barkwancin mu, na kamu da soyayya.
Bayan duk wannan lokacin, har yanzu kana da ban mamaki. Ina jin daɗin samun ka a rayuwata.
Kowane labarin soyayya yana da kyau, amma namu shine wanda da na fi so. Ba zan iya jira in ga abin da rayuwa ta tanadar mana tare ba!
A duk lokacin da nake tare da kai, Ina kara fahimtar cewa ina yin abu ɗaya da na gaya wa kaina ba zan sake yi ba... Itace faɗawa soyayya.
Ka dauke numfashina. Ba zan iya tunanin rayuwa ta ba tare da kai a gefena ba. Na gode da kasancewar mai ban mamaki a wannan tafiyar!
Na san mu matasa ne kuma ya yi da wuri a faɗi wannan...amma, ina fatahn kai ne dai daga karshe.
Kirana da fure yana da kyau, kirana da sarauniya yana da kyau. Amma kirana naka shine abin da nake so da gaske.
Na gode da soyayyar ka da ta sa na ji kamar na fi kowa kyau a duniyar nan.
Wani lokacin sai in rufe idona in gode wa Allah da ka zo rayuwata. Kana da albarka sosai.
Kana bani irin tunanin da mutane da dama ke rubuta litattafai akai. Godiya nake.
A duk lokacin da na saurari zuciyata, sai inji tana raɗa sunan ka.
Haɗuwa da kai ya kasance kamar sauraron waƙa a karon farko da sanin cewa zai zama wanda na fi so.
Da na ganka sai na ji tsoron haɗuwa da kai, da na haɗu da kai sai na ji ina tsoron faɗawa soyayyar ka. Yanzu da ina son ka, ina tsoron rasa ka.
Ko da yake ba zan iya ganinka sau da yawa kamar yadda nake so ba, kai ne tunani na na farko da na ƙarshe a kowace rana da kowane dare. Ina kewar ka alnuri.
Sau biyu ne kawai nake so in kasance tare da kai. Yanzu, da kuma Har abada.
Kalaman So Masu Ratsa Jiki
Na san yadda nake ji a gare ka gaskiya ne domin na fi yawan lokacin tunanin ka fiye da kaina.
Na yi imani da gaske da cewa mafarki na iya zama gaskiya saboda nawa ya zama a lokacin da muka haɗu. Ba zan taba barin ka ba, masoyina!
Tunanin ka yana sa ni a farke. Mafarkinka yana sa ni barci. Kasancewa tare da kai yana raya ni.
Sau da yawa, dan dole neke tsungulan kaina idan na gan ka kusa da ni. Kai ne cikar burina.
Na kasance ina tunanin ka duk yini. Yanzu kai ma ka rike mafarkan da nake yi. Bana kuka saboda ina son ƙaunar ka.
Na san a karo na farko da na haɗu da kai cewa akwai wani abu game da kai da nake bukata. Abun mamaki sai ya zama ba wani abu bane game da kai bane, Kai ne kawai.
Kana cikin Tsoka na, da jinina da kuma zuciyata. Dole sai na farka kaina kafin na iya barinka ka tafi.
Ƙauna ita ce yanayin da farin cikin wani ya zama mahimmanci ga naka.
Ni ba mai addini ba ne, amma wani lokacin ina tunanin cewa Allah ya yi ka ne a don ni.
Ina son komai game da kai. Kai ne ainihin yarjejeniyar; ko da yaushe kana a shirye, ko da yaushe so. Ina son ka daga zurfafan zuciyata, yarimana mai fara'a.
Kai, ni ce yarinyar da tafi kowa sa'a a duniya saboda ina da mafi kyawun namiji a rayuwata. Ina godiya gare ka da canza rayuwata, kuma ina son ka sosai.
Zuciyata naka ce don kauna, ƙauna da ƙauna har abada, kuma ina farin cikin kiran ka nawa a yau da kullum. Ina sonka fiye da yadda kake tunani ya kai saurayi na.
Lu'u-lu'u da zinare ba su da daraja idan aka kwatanta da ƙaunar da nake ma. Ƙaunar ka ita ce mafi daraja a gare ni. Ina son ka sosai.
Mun yi doguwar tafiya mai nisa, kuma wannan hanyar ta kasance duk abin ban mamaki. Ina so in ci gaba a kan wannan hanya tare da kai har abada.
Lokacin da ka fahimci kana son yin sauran rayuwar ka tare da wani, kana son sauran rayuwar ku ta fara da wuri-wuri.
Na ga cewa kai cikakke ne, don haka na ƙaunace ka. Sai na ga ba ka kamala ba, sai naji ma na ƙara son ka.
A duk duniya babu zuciya gare ni kamar naka. Kuma A duk duniya babu soyayyarka irin tawa.
Ƙaunata gare ka ba ta da iyaka; iyakokinta suna kara fadada. Ƙaunata da rayuwata tare da kai zai zama labari mara ƙarewa.
Duk da cewan babu kai a gefe na, amma ina jin gaɓanka, yana cuɗanya da ni. Ina son ka sosai, masoyi.
Na gode da amincewar zuciyar ka a gare ni. Na yi alkawari zan kula da shi kuma ba zan taɓa ɗaukar ka da wasa ba.
Kalaman So na Ban Dariya
Ina tsammanin kuna fama da rashin bitamin ni.
Ina son ka. Kana ɓata min rai fiye da yadda na zata yiwu. Amma ina so in yi amfani da kowane minti mai ban haushi tare da kai.
Kullum ina kara soyayyar ka. Amma banda jiya, jiya ka kasance mai kyakkyawa ban haushi.
Na yi alkawarin son ka, na mutunta ka, da tallafa maka, kuma fiye da komai, ka tabbata ba kawai ina yin wannan magana bane saboda iɓa jin yunwa.
Ina son ka da dukkanin jaka na. Da nace zuciya, amma jakata ta fi girma. Hhhhhh!
Ka san wannan jin daɗin da kake samu a lokacin da kake son wani? Hakan yana nufin hankalin ka ya bar jikin ka.
Kuna son furanni, amma kuna yanke su. Kuna son dabbobi, amma kuna cin su. Ka ce mani kana so na, don haka yanzu na ji tsoro!
Kai mai sihiri ne? Domin duk lokacin da na kalle ka, sai naga kowa ya bace!
Yana da ban mamaki yadda wata rana wani zai shiga cikin rayuwar ka, sannan washegari sai kaji ba za ka iya rayuwa ba tare da shi ba.
Ka zamo kamar ƙamus - kana ƙara ma'ana ga rayuwata.
Ka sace mun zuciyata don haka nake shirin ramawa... Zan dauke maka sunan ka na karshe. Kaima kaji inda daɗi!
Kana da duk abin da zan taɓa buƙata: makamai masu ƙarfi, zuciya mai ƙauna, da injin daskarewa cike da ice cream!
Dangantakarmu tana kan ƙa'idodi guda biyu masu sauƙi. Na daya, ka yi duk abin da na fada. Na biyu, kar a manta lamba ta farko.
Ina son ka ko da ka kasance mai tonon faɗa wani zibin.
Wai cin kana jin yarda nake ji kuwa? ji kaina nake tamkar mahaukaciya yayin da na tuna da kai.
Allah sarki na sace wa wani zuciyar sa. Kayi haƙuri don ta riga da ta zamo nawa har abada!
Wai ka san me nake jin yi daddaren nan? Kawai ji nayi ina son na mari ƙumatun ka!
Ina son na zama dalilin da zai sa ka kalli wayar ka ka ɗago da murmushi, sannan ka haɗa kai da pole hhhhh!
Wani lokaci ina mamakin yadda kake iya jure mani. Sai na tuna, Ashe ni ke juriyan! Har kan ka Yayi girma!
Wani ciwon kai ne ya dame ni tun da rana, ashe raban da na sa ido na a kan ka kenan!
Kalaman So na Kewa
Ina ƙara soyayya kaɗan duk lokacin da na gan ka kuma ba zan iya jira in sake ganin ka ba. Ina kewar ka sosai!
Ina kewar ka. Wataƙila ba koyaushe nake nuna shi ba, wataƙila ba koyaushe nake gaya wa mutane ba, amma a ciki, Ina kewar ka kamar hauka.
Ƙewar mutum bangare ne na son shi. Idan ba ku rabu ba, ba za ka taɓa sanin ainihin ƙarfin ƙaunarku ba.
Ba zan iya fitar da kai daga raina ba. Wataƙila ya kamata ka kasance a wurin.
Tunanin ka kowane; na Sakan, minti, awa, rana, magani ne ga rashin lafiyata na rashin ka a gefe na.
Rashin ka tamkar yawo ne ba tare da zuciyata ba. Ina jin haka domin har yanzu zuciyata tana tare da kai.
Yana da wuya lokacin da kuka rasa mutane. Amma kun san idan kun rasa su, wannan yana nufin kun yi sa'a. Yana nufin kana da wani na musamman a rayuwarka, wanda ya cancanci ƙewa.
Na daina magana da kai don ka rasa ni, amma a ƙarshe, ni ne wanda ke kewar ka fiye da kowane lokaci.
Ba za ka taɓa barin raina ba. Ba ma lokacin da nake da abubuwa miliyan da zan yi tunani akai ba.
Na yi kewar ka sosai, da rashin fahimta, da rashin hankali, da mugun nufi.
Wataƙila za ka iya fita daga gani na, amma ba za ka taɓa iya fita daga zuciya ta ba.
Na yi kewar ka da har ina kishin mutanen da ke samun damar ganin ka kowace rana a inda kake.
Duniya ba ta zama iri ɗaya a duk lokacin da ba ka kusa da ni.
Lokacin da na gaya muku cewa zan yi kewar ku, ba yana nufin ba zan taɓa shawo kan ku ba. Yana nufin kawai ina fata dama bai zama dole ba ne.
Rasa ka yana samun sauki a kowace rana domin na yi gaba da ranar karshe da na gan ka, kuna ina kara kusa da ranar da za mu sake haɗuwa.
Ban damu ba ko minti 5 ne ko dare duka, ina son ganin ka ne kawai.
Faɗuwar rana a nan yana da ban mamaki, amma zuciyata tana zafi saboda ba zan iya jin daɗin su da kai ba.
Kana sanin wani ya kasance na musamman a gare ka a lokacin da kwanaki ba suyi daidai ba tare da shi ba.
Soyayya yakan sa a rasa wani a duk lokacin da akayi rabuwa, amma ko ta yaya ina jin dumi a ciki saboda muna kusa a zuciya.
Bani taɓa son yin wuni ɗaya ba tare da kai ba.
Kalaman So Masu Sa Tunani
Na yi mafarkin gaske game da kai a daren jiya…
Lokaci na gaba da zaka zo, ina da abin mamaki a gare ka.
Ba zan iya daina tunanin wannan mutumin ba. Ina tsammanin za ka iya saninsa.
Ƙawaye na sun gaya mani suna so mazajen su su kasance kamar ka.
Kowa na tambaya ta dalilin da yasa nake samun murmushi akai-akai akan fuskata. Ko kana da masaniya?
Na runguma matashin kaina da na farka da safen nan, Da ma ace kaine.
Aiki yana tafiya a hankali, amma tunanin ka yana sa yayi sauri.
Me kake tunani zan yi idan kana nan kusa da ni a yanzu?
Cikina yana yin ɓacin rai yana tunanin duk nishaɗin da za mu yi a firan daren yau.
Ka kasance a raina duk yini. Ba zan iya mayar da hankali kan komai ba.
Mafarke- mafarke na na zuwan mun da kyau saboda koyaushe kana cikin su.
kana ganin zaka iya zuwa gidan mu yau? Ina da wani abu na musamman da na shirya maka.
Ina soyayya da wani. Yana da idanuwa na mafarki, yana huci cikin shawa, yana murmushi yana kuma karanta sakona a yanzu haka.
Shin akwai wanda ya taɓa gaya maka cewa kana da dariyar da aka iya kamuwa tamkar cuta? Ba zan iya taimakawa ba sai ƙara soyayya a duk lokacin da na ji ta.
Kafin in san ka, ina tsammanin babu wanda zai iya zama cikakke. Hakika Allah ya halicce ka da yawan tunani da kulawa.
Har yanzu ina blushing. Kana son sanin dalili?
Inda ace ana biya na sisi a duk lokacin da na yi tunanin ka, da na zama biloniya nan ba da jimawa ba.
Ji nake kamar na haukace, duk inda na kalla kai nake gani.
Ina kallon duk hotunanmu tare, ina tunawa da lokutan ban mamaki. Ba zan iya jira don ƙirƙirar ƙarin irin waɗannan abubuwan tunawa tare da kai ba.
Na kamu da ƙamshin ka, da ɗanɗanon ka, da jin daɗinka, da ma kai duka. jarabawa ce guda ɗaya da ban taɓa son sakinta ba.
Gabatarwa
Shin zafafan kalaman soyayya da muka lissafa muku a sama suna da dadin ki? Toh kuyi zabi daga cikin zafafan kalaman soyayya masu nishadantarwa da ratsa da muka jera maku. Shin kuna da wasu kalaman so da kuke ganin ya kamata wasu su sani? Toh mu ji mana!
Comments
Post a Comment