Shin kuna neman sakonnin soyayya dan tura wa masoya da daddare? Koh mun rubuto maku su. 100 farko na mata ne dan tura was samarin su. 100 karshe kuma na samari ne dan tura wa budurwan su. Sakonnin Soyayya na Dare Zuwa ga Saurayi Hubbina, barka da wannan lokaci. Nasan yadda nake cikin tinaninka, kaima haka kana cikin tinanina. Ka kula mun da kanka kulawa sosai. Duk sanda nake kallon taurarin cikin samaniya, tinanin soyayyar danake maka kawai nakeyi. Ka nuna mun so ta gaskiya fiye da yadda nake tinani. Ka rabani da abunda da zai hanani sonka, ka hadani da dalilan da zasu sa na soka. To sadaukin maza, Ina kaunar ka. Duk lokutan da muke tare, farin cikina ninkawa yakeyi fiye da na baya. Sai nayi kokarin boyewa farin cikin amma kuma fuska bata amincewa da hakan. Bansan mene ke damuna ba, bantaba jin kewarka kamar yadda nakeji ba yau, inda ace muna tare, daka gane irin kaunar da nake maka. Rayuwata na cikin wani yanayi na nishadi soboda farin cikin da kazo mun da ita. Ruhina, tunda kataf